28 Satumba 2021 - 07:47
​Rasha: Lavrov Ya Ce Mali Ta Bukaci Taimakon Wani Kamfanin Tsaro Na Kasar Rasha

Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa gwamnatin kasar Mali ta bukaci taimakon wani kamfanin tsaro na kasar Rasha don yaki da ‘yan ta’adda a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya ce Lavrov ya bayyana haka ne a jiya Asabar a majalisar dinkin duniya. Ya kuma kara da cewa yana ganin kasar Mali ta dauki wannan matakin ne don kasar Faransa ta na son fidda sojojinta daga kasar.

Daga karshe ministan ya ce babu ruwan gwamnatin kasar Rasha da wannan yarjejeniya ta Mali da kamfanin tsaro mai zaman kansa na kasar.

Kafin haka dai firai ministan kasar ta Mali Choguel Maiga ya fadawa babban zauren MDD kan cewa kasar Faransa ta yi watsi da su don haka su na neman wanda zai maye gurbinta.

Gwamnatin kasar Faransa da kuma tarayyar Turai sun fadawa sojoji masu mulkin Mali kan cewa ba zasu taba hana kasa guda da jami’an tsaro na kasar Rasha ba, sannan sun kara da cewa ida gwamnatin kasar Mali ta kuskura ta ci gaba da wannan shirin to zata yi nadama.

342/